Main menu

Pages

Wani mutum ya kashe iyalan sa harsu bakwai

 

WANI MUTUM YA KASHE IYALAN SA HARSU BAKWAI

Wani mutum Dake kasar Amurka ya kashe iyalan sa guda bakwai. Wannan labari ya zamo abin tashin hankali a wajen mutanen da yakin da abin ya faru.

Jami'an tsaro na birnin Utah inda abin ya faru sun bayyana cewa sun gano gawarwaki har guda bakwai da magidancin ya kashe kafin daga bisani shima ya kashe kansa.

Wannan abu ya faru ne biyo bayan sabani da magidancin ya samu tsakanin sa da matar sa kafin yin kisan. Magidancin ya dauki wannan mataki bayan da matar tasa ta shigar da Karansa tana mai Neman kotu ta raba auren su.

An bayyana sunan magidancin mai shakaru 42 da Micheal Height da matarsa mai suna Tausha yar shekara 40.

A cikin kisan magidancin ya hada da sirikarsa yar shekara 72 da Kuma yayan guda biyar uku mata biyu maza.

Jami'an tsaron sun bayyana cewa duka gawarwakin an samesu da raunikan bindiga Wanda ke nuna da ita akayi amfani wajen aiwatar da wannan aika-aika.

Wata kawar Tausha dake dake bada bayani tace kawar tata mutuniyar kirki ce bata da matsala da kowa kuma macace mai kokarin yin abu iya karfinta. Kuma bata rikon kowa ballantana har a sami sabanin da ita.


 

Comments