Ba sarake ya rasa rawanin sa na matsayin waziri a Bauchi.
Wannan lamari ya faru ne a jahar Bauchi dake arewacin najeriya. Gwamnatin jahar Bauchi ta rawaito cewa dalilin da yasa ta sauke wazirin na Bauchi wato Alhajin Bello Kirfi daga kan mukaminsa na wazirin Bauch.
Gwamnatin jahar Bauchi tace tsohon wazirin bayan martaba girman mukamin sa na matsayin wazirin sarki dake masarautar yana zubar da girmansa a inda bai kamata ba ita Kuma taga bazata iya zuba masa Ido ba yana zubar musu da kima da mutuncin masarauta ta a idon Duniya.
Amma daya bangaren wazirin yana zargin gwamnati ne da tsanar sa saboda yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa a jam'iyar pdp wato Alhaji Atiku Abubakar.
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya na jahar bauchi wato Hon. Abdurrazak Nuhu Zaki ya karyata lamarin ga manema labarai. Kuma ya Kara da cewa hasalima gwamnan jihar bauchi ne da kansa yasa aka kafa kwamitin na yakin neman zaben jam'iyar PDP tin daga matakin shugaban kasa har zuwa matsayin kansilan kana Nan hukumomi.
Dalilin da yasa Gwamnatin jahar Bauchi ta tube rawanin wazirin Bauchi.
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya na Bauch Hon. Abdurrazak Nuhu Zaki yaci Gwamnatin ta dau wannan hukuncin ne saboda wazirin yana maganganu da basu dace ba a wararen dabai kamata ba.
Kwamishinan ya Kara da cewa wannan ba karo na farko bane da ake sauke wazirin daga mukamin sa ba na wazirin Bauch. Ko da a baya an tana sauke shi saboda irin wannan halaye nashi Kuma kwamishinan yakara da cewa wannan lamari bashda nasaba da siyasa, kawai munaso mukare martabar Gwamnatin mu dakuma masarautun mu na gargajiya.

Comments
Post a Comment