Main menu

Pages

Wata Sabuwa: Messi zai koma wata gungiyar kwallon kafa dake kasar Saudia

 

Wata Sabuwa: Messi zai koma wata gungiyar kwallon kafa dake kasar Saudia

Wata Sabuwa: Messi zai koma wata gungiyar kwallon kafa dake kasar Saudia

Wata kungiyar kwallon kafar saudiya na zawarcin Messi.

Bayan da kungiyar kwallon kafar Al-nassr FC dake saudiya tayi awon gaba da Cristiano Ronaldo a watan daya gabata.

Ana cikin haka Kuma kwatsam aka sake samun bayyanar wata kungiyar kwallon kafa dake zawarcin shahararren dan wasan kwallon kafar nan dan kasar Argentina wato Lionel Messi.

Kungiyar mai sunan Al-hilal ta nemi da wasan da yazo ya Rika buga mata wasa  akan dala miliyan 350 ($350).  Hakan ya biyo bayan wani hadin gwiwa da gwamnatin kasar tayi nason samun karuwar masu shiga kasar domin yawon buda Ido. 

Kamar yadda hasashen masana ya nuna gwamnatin kasar saudiya ta yanke hukuncin hakan ne domin samun masu zuwa budar ido zuwa kasarta su karu. Wanda take ganin hakan zai matukar taimaka mata wajen samun damar karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta Duniya a shekara 2030.

Amma kafin nan kungiyar kwallon kafar ta saudiya tana bukatar bukasa kwallon kafar ta a cikin gida. Hakan  yasa kungiyar kwallon kafa ta Al hilal take zawarcin Messi domin kwarzon dan wasan yasake zama abokin hamayyar Cristiano Ronaldo wanda suka dade suna fafatawa da juna a bangaren duniyar kwallon kafa.

Wannan kungiyar da take neman gwarzon dan wasan ba wata bace face, gungiyar kwallon kafa ta Al hilal wace take abokiyar hamayya a bangaren kwallon kafa dake saudiya.

Ita dai wannan gungiyar kwallon kafar ta yiwa  messi tayin kudi har dala miliyan dari uku da hamsin ($350) Wanda kwantaragin zai kasance na iya tsawon shekara daya, duk da yake abu ne mai wahala mutum ya tsallake irin wannan makudan kudin.


You are now in the first article

Comments